Kungiyar Shi’a Ta Nemi Kasashen Duniya Da Su Makalawa Najeriya TakumKumi



Kungiyar Shi’a ta Nijeriya ta nemi kasashen duniya kan su Kakabawa Nijeriya takunkumin karya tattalin arziki idan har gwamnatin tarayya ta ki mutunta umarnin kotu na Sakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim El Zakzaky.
Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiya, Abdulhameed Bello ya ce kungiyar ba za ta bi hanyar tayar da hankali wajen cimma burinta na sako Shugabanta inda ya jaddada cewa ‘yan Shi’a mutane ne da ke son zaman lafiya sabanin yadda gwamnati da yawancin al’umma ke fahintarsu.

You may also like