A wani mataki na yin raddi ga Shugaban Kasa a sakonsa na sabuwar shekara, Mabiya Kungiyar Shi’a ta kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan ya mutunta hukuncin kotu wadda ta bayar da umarnin Sakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim E Zakzaky a maimakon zagaye- zagaye da batun.
Mai Magana da Yawun Kungiyar, Ibrahim Musa ya ce sun yi mamaki yadda Buhari ya bayyana su a matsayin ‘yan uwansa a cikin jawabin nasa bayan a can baya ya dauke su a matsayin ‘yan aware. A jiya ne dai, Shugaba Buhari ya nemi ‘yan Shi’a kan su daina tayar da zaune tsaye tare da mutunta dokokin kasa.
A nasa bangaren, Mai taimaka wa shugaban Najeriya na musamman kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce, bai kamata ‘yan Shi’a su zargi Buhari ba kan kin sakin shugabansu, Sheikh El-zakzaky ba.
Ya ce duk da cewa kotu ta yanke cewa a saki Sheikh Zakzaky amma kuma akwai wasu da suka shigar da daukaka kara kan batun.
Ya kuma kara da cewa baya da batun daukaka kara akwai kuma wasu rahotannin tsaro da hukumomin tsaron kasar su ma suke dogara da su.
Malam Garba Shehu ya ce, ya kamata ‘yan Shi’ar sun sani cewa Buhari ba shi da hannu a shari’ar da ake yi wa shugaban nasu.
Sannan kuma ba shi da hannu kan kwamitin bincike da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wanda ya ba da shawarar haramta kungiyar.
Daga karshe malam Garba ya shawarci mabiya mazhabin na Shi’a su jira abin da shari’a za ta yanke nan gaba.
Kungiyar ‘yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi’a dai ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky kamar yadda kotu ta ba shi umarni maimakon kiran da ya yi musu na su zauna lafiya.
A jawabinsa na sabuwar shekara Shugaba Buhari ya ce, “A matsayinsu na ‘yan uwanmu, muna kira ga ‘yan Shi’a su rungumi turbar zaman lafiya. Dole su bi dokokin kasar da suke zaune a ciki”.
Ya kara da cewa, “A lokaci guda kuma, dole jami’an tsaro su rika mu’amala da su ta hanyoyin da suka dace da kuma bin doka kan yadda suke tunkararsu”.