Kungiyar Tuntubar Arewa Ta ACF Ta Tattauna Kan Batutuwan Tsaro, Yajin Aiki, Da Ambaliyar Ruwa
KADUNA, NIGERIA – Kungiyar ta ACF wadda ta gudanar da babban taronta na zangon karshen shekara a garin Kaduna, ta ce akwai bukatar samar da ayyukan yi ga matasa don magance matsalolin tsaro a yankin Arewa, kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar kuma wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Muhammad Ida ya bayyana wa Muryar Amurka.

Sanata Muhammad ya kuma ce, ya kamata a yaba wa gwamnati saboda korinta kan sha’anin tsaro. Sannan yayin da babban zaben kasar ke tafe a shekarar 2023, ya kamata gwamnati ta tabbatar an yi zaben lafiya an kuma ba jama’a zabinsu.

Shi kuwa babban Sakataren kungiyar ta ACF Malam Murtala Aliyu, cewa yayi cikin batutuwan da aka tattauna akwai masu muhimmanci da ya kamata gwamnati ta lura da su, musamman matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a sassan jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto inda ‘yan bindiga ke kai hare-hare suna satar mutane don neman kudin fansa.

Aliyu ya kara da cewa akwai kuma batun ambaliyar ruwa da ta shafi wasu yankunan Arewacin Najeriya a bana, inda dubban mutane suka rasa matsugunnansu, ya kamata gwamnati ta dauki matakan da suka dace ta kuma tallafa wa wadanda bala’in ya shafa.

Batun matsalar dogon yajin aikin malaman jami’o’i na daga cikin abubuwan da wasu mahalarta taron suka koka akai.

Aishatu Yakubu Maijama’a, ita ce mataimakiyar shugaban kungiyar ACF reshen jihar Kano, ta ce duk kasar da babu ilimi matacciyar kasa ce, kuma bai kamata a ce an zuba ido ana kallon matsalar ba.

Babban taron kungiyar tuntubar na kungiyar ACF ya zo daidai da ranar malamai ta duniya da ta ci karo da yajin aikin malaman jami’a a Najeriya da ke neman lashe zangon karatu uku a jere.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

You may also like