Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta(INEC) ta tabbatar da cewa kimanin kungiyoy 60 ne suka gabatar da bukatar a yi masu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.
Da yake karin haske game da batun, Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar INEC, Rotimi Oyekanmmi ya ce tuni hukumar ta fara tantance kungiyoy inda ya kara da cewa akwai wasu kungiyoyin takwas da su ma ke shirin mika irin wannan bukata.