Kungiyoyi sun yi tayin taimakawa a tattauna da Boko Haram


 

Wasu kungiyoyi sun yi tayin taimakawa gwamnatin Najeriya, wajen tattaunawa da mayakan Boko Haram, domin musayar ‘yan makarantar Chibok da suke rike da su, da kuma wasu daga cikin fursunonin mayakan.

Mai bawa shugaban Najriyar shawara kan kafafen yada labarai malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da manema labarai.

Cigaban na zuwa ne bayan da shugaban Najeriyar Muhdu Buhari, a lokacin wani taro a kasar Kenya watan da ya gabata, ya ce a shirye Najeriyar ta ke, ta tattauna da Mayakan ta hanyar wakilcin manyan kungiyoyin kasa da kasa daga bangaren Boko Haram din.

Wani masani kan yaki da ta’addanci a Najeriyar dakta Ameachi Nwoakolo, ya ce musayar ‘yan matan da fursunonin mayakan bai sabawa ka’aida ba, kasancewar mataki ne da dukkan kasashen duniya ke dauka.

Yanzu dai lokaci ne zai nuna tabbatuwar fara wannan tattaunawa.

You may also like