Kungiyoyin agaji na waje sun dakatar da aiki bayan Taliban ta hana mata aiki da suWasu mata a Afghanistan

Asalin hoton, EPA

Manyan kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje uku sun dakatar da ayyukansu a Afghanistan bayan Taliban ta haramta wa mata yi musu aiki.

A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, kungiyar Care International, da ƙungiyar agaji mai zaman kanta ta ƙasar Norway (NRC), da kuma Save the Children sun ce ba za su iya ci gaba da ayyukansu ba “ba tare da ma’aikatanmu mata ba.”

Kungiyoyin agajin sun kuma “bukaci” a bar mata su ci gaba da yi musu aiki.

Shugabannin Taliban da ke mulki a Afghanistan na ci gaba da abin da ake ganin tauye hakkin mata ne.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like