Kungiyoyin kwadago sun gargadi gwamnatin Najeriya kan sayar da kadarori


 

 

 

Hadakar kungiyoyin kwadago a Najeriya, ta bukaci gwamnatin kasar, da ta yi watsi da shirinta na sayar da kadarorinta don kauce wa haddasa tashe-tashen hankula.

Kungiyoyin da suka hada da NLC da TUC da NUPENG da PENGASSAN sun yi amfani da murya guda wajen bayar da gargadin, a wani taro da suka gudanar a wannan litinin a birnin Abuja.

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Ayuba Wabba ya shaidawa Sashin Hausa na RFI cewa, daya daga cikin madogarar da taron yayi amfani da ita wajen daukar matakin, shi ne la’akari da rashin alfanu da irin wannan yunkuri ya haifar a baya.

Wabba ya ce saida kamfanin samar da hasken wutar lantarki babban misali ne, ganin yadda har yanzu bayan sayar da shi kwalliya bata biya kudin sabulu ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like