Kungiyoyin ‘Yan Sa Kai Ta Kashe Gobara Na Da Muhimmanci A Kasuwanni-OlolaYa kuma alakanta yawaitar asarar dukiyoyi da rashin hanyoyin da za su baiwa jami’an agajin gaggawa damar shiga kasuwar domin kashe gobarar.

A cikin wata guda an samu tashin gobara daban-daban guda uku a manyan kasuwanni da kuma shaguna hada da sansanonin ‘yan gudun hijira guda biyu wanda suka auku a jihar Borno. Sai dai wadda ta fi girma itace wacce ta auku a kasuwar Litinin da aka fi sani da Monday Market inda aka yi asarar sama da shaguna dubu 12 da wutar ta kurmus.

Borno Burnt Market 3

Borno Burnt Market 3

Abdulganiyu ya ce idan da masu aikin sa kai sun samu horo yadda ya kamata tare da samar musu da kayan aikin kashe gobara, za su dakile wuce gona da iri da gobarar ta yi tun kafin isowar jami’an kashe gobara.

“Hanya daya tilo da za a iya hana gobara ita ce tabbatar da cewa an samar da mafi saukin na’urori. Tunkunyar kashe gobara (Fire Extinguisher) a kowane dayan wadannan shagunan na iya taimakawa sosai don rage aukuwar gobara.

Bornon Burnt Market 2

Bornon Burnt Market 2

“Kananan horo kan yadda ake amfani da kayan aiki yana da mahimmanci a koyaushe saboda yawancin wuta yana farawa kadan, ba babba ba, kuma idan ba ku san abin da za ku yi ba, yana karuwa,” in ji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba jami’an sa za su fara horas da ‘yan kasuwar aikin sa kai kan yadda ake amfani da barguna da na’urorin kashe gobara.

Wasu ‘yan kasuwa da gobarar ta lakume dukiyoyin su sun yi kira ga gwamnati da ta tallafa musu wurin farfado da kasuwanci musamman a cikin wannan wata azumi kana wasu suka ce gwamnati ta gaggauta gyaran kasuwar.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu cikin sauti daga Maiduguri:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like