
Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmad Tijjani Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Twitter,
- Aiko rahoto daga Abuja
Goman ƙarshe na azumin watan Ramadan, lokaci ne mai muhimmancin gaske ga Musulmai.
Wasu malamai ma na da ra’ayin cewa ya fi farkon watan, musamman ga waɗanda ke son ƙara kusantar Allah (SWT).
A goman ƙarshen Ramadan ne kuma ake ƙara yawaita ibadu musamman ma sallolin dare.
Malamai sun kuma ruwaito cewa idan aka shiga goman ƙarshe, Manzon Allah (SAW) yana ƙara ɗaura ɗamara da kuma jajircewa wajen yawaita ibada.
Raya dare, abu ne da ke ƙara kusanci da Allah, inda duk abin da mutum ya roƙa kan iya samun dace saboda alfarmar watan Ramadana.
A lokacin ne kuma Musulmai da yawa ke zurfafa ibada ta hanyar sallar tahajjud da shiga ittikafi, wasu kuma sukan tafi Umrah, yayin da wasu kan tsaya a gida suna yawaita addu’o’i a lokacin goman ƙarshe.
Sai dai duk da wannan yunƙuri da rububin gudanar da ayyukan lada, akwai kuma wasu kura-kurai da aka lura Musulmai na yi a wannan lokaci na goman ƙarshe.
Kan haka ne, BBC ta tattauna da wasu malamai don sanin ko waɗanne kura-kurai ne.
Barin farilla a yi mustahabbi
Sheikh Nuru Khalid, wani fitaccen Malami a babban birnin Najeriya, Abuja, ya ce za ka ga mutum yana tashi cikin dare yana ibada amma sai ya kwanta ya kasa tashi don yin sallar asubahi.
Malamin ya ce hakan bai kamata ba, saboda barin sallar farilla a kan lokaci kuma a cikin jam’i, abu ne da Allah (SWT) ba Ya so musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadana.
Sheikh Nuru ya gargaɗi mutane masu irin wannan ɗabi’a da su daina.
Kuma su tabbatar suna sallar farilla a kan lokaci don samun rabauta wajen Allah Maɗaukakin Sarki.
Wasa da aiki
Sheikh Nuru Khalid ya ce akwai wasu mutane musamman ma’aikata waɗanda ke matsawa wajen tsayuwar dare, amma kuma sai su makara zuwa wurin aiki.
“Wannan gaskiya ba daidai ba ne”, in ji malamin na Abuja.
Ya ce wasu ma’aikata kuma idan sun je wuraren aiki sai su ɓuge da barci har ta kai ga ana ba su takardar gargaɗi saboda rashin mayar da hankali.
A cewarsa, wannan ba ɗabi’ar kirki ba ce kuma bai kamata a samu Musulmin ƙwarai yana aikata wani abu mai kama da cin amanar aiki ba.
Kamata ya yi in ji malamin, mutane su guje wa irin waɗannan kura-kurai sannan su tabbatar sun yi komai bisa dacewa, ba tare da an samu matsala a wajen ibadarsu da kuma wurin ayyukansu ba.
Tafiya Umrah
Duk da yake, abu ne mai kyau zuwa Umrah a cewar malamai kamar Sheikh Nuru Khalid musamman ma a wannan lokaci na azumin watan Ramadana, amma abin da wasu ke yi, kafin su tafi da kuma bayan sun je, abubuwa ne da ba su kamata ba.
“Mutum ya matsa wa kanshi, ya haɗa ƙarya da gaskiya, ya haɗa kuɗin Umrah ya tafi, wannan ba daidai ba ne,” in ji Malamin.
Ya kuma ce akwai mutanen da suke zuwa umrah su yi ta yawace-yawace da saye-saye, su miƙe ƙafa su yi barci.
Ana kuma ta ɗaukar hotuna ba tare da sun haɓɓaka ibadarsu ba, a lokacin da suke Ƙasa mai Tsarki, abu ne da ya ce bai dace ba kwata-kwata a addini.
Malamin ya ƙara da cewa akwai kuma wasu mutane da ke ɗiban kuɗi su tafi umrah, amma a kusa da su akwai talakawa da ke cikin yunwa, ba su da hatta abin da za su ci.
Sheikh Nuru Khalid ya ce taimaka wa makwabta da abin da za su ci a lokacin azumi, shi ne abin alheri mafi dacewa.
Rage ƙoƙari wajen ibada
Wani kuskure da wasu Musulmai ke yawan yi a goman ƙarshe cikin watan Ramadana, shi ne rage ƙoƙari wajen ibada.
Duk da yake da yawan Musulmai na ƙara zage damtse a wannan lokaci, amma akan samu wasu mutane da kan yi rauni idan azumi ya taho ƙarewa, saɓanin yadda suka faro ibada gadan-gadan da ƙaurace wa saɓo a farkon watan, kamar yadda Dakta Hussaini Zakariyya, shi ma wani fitaccen malami ya bayyana.
Ya ce a daidai irin wannan lokaci ne Manzon Allah yake ƙara himma a ibada, “amma sai ka ga mutane na rage kuzari wajen bauta wa Allah.”
Ya ce kamata ya yi mutane su guji aikata hakan, inda ya ce abin da ya kamace su a goman ƙarshe, shi ne dagewa kan ibadu don samun dacewa wajen Allah (SWT).
Cin abinci da yawa lokacin buɗe-baki
Dakta Hussaini Zakariyya, ya kuma ce mutane suna yawan aikata kuskuren cin abinci ko shan ruwa fiye da ƙima lokacin yin buɗe-baki, inda ya ce hakan zai sanya su samu kasala ta hanyar kasa tashi su yi salloli da daddare.
Malamin ya ce abin da ya kamaci mutum a lokacin yin buɗe-baki shi ne cin abinci daidai gwargwado wanda ba zai hana mutum yin ibada ba.
Ya ce mutane su mayar da hankali wajen yin ibada a kwanakin goman karshe na watan azumi saboda ba kowa ne zai samu damar sake ganin watan ba sai wanda Allah ya kaddara zai gan shi.
Ɓata lokaci wajen girke-girke
Dakta Zakariyya ya ce mata na da ɗabi’ar ɓata lokaci wajen yi wa mazajensu girke-girke, inda hakan ke hana da yawa daga cikinsu yin ibada musamman ma a lokutan goman karshe na azumi.
“Akwai wasu mata da za ka gansu a kicin har sallar Magriba ta fara wucewa da sunan za su burge mazajensu, wannan bai dace ba,” in ji Malamin.
Ya ce kamata ya yi su fara girki da wuri don su kammala a kan lokaci da kuma ganin sun samu damar yin ibada domin samun rabauta.
Malamin ya ce duk rintsi, su tabbata ba su yi wasa da ibada ba, inda ya ce kada wajen kokarin bauta wa miji, ya sa su manta da bautar Allah (SWT).
Malamai sun hori mutane da su dage wajen yin ibada musamman a kwanakin goman karshe na watan azumin ba tare da nuna gajiyawa ba.
Sun ce muddin mutum ya rinƙa raya dararen goman karshe na watan azumi suna masu tawassali, to ba shakka Allah (SWT) Zai yafe musu zunubansu tare kuma da biya musu bukatunsu na alheri.