Kura ta fara lafawa a Gabon


Shugaba Ali Bongo da kasashen duniya sun bukaci karshen zanga-zangar da ke ci gaba da daukar zafi a kasar Gabon.

An dai share yinin ranar Alhamis ana dauki ba dadi tsakani masu zanga-zangar nuna adawa da zaben Ali bango da kuma jami’an tsaro a birnin Libreville dama a wasu sauran biranen kasar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu. Ministan cikin gida na kasar Gabon Pacome Moubelet ya ce kawo yanzu sun kama mutane sama da dubu 600 a birnin Libreville da wasu kimanin 300 a sauran yankunan kasar sannan sun kwace gurneti da bindigogi kirar AK-47 a hannun masu zanga zangar. Shugaba Ali Bango ya bukaci hadin kan ‘yan adawan kasar dan kawo karshen tashin hankali da kasar ke fama da shi.

Gipfel Afrikanische Union Addis Abeba Madugun ‘yan adawa a Gabon, Jean Ping

Sai dai har kawo yanzu ba a san inda madugun ‘yan adawar wato Jean Ping ya ke ba tun bayan da sojoji suka kai hari a Hedikwatar jam’iyar sa a yammacin ranar Laraba biyo bayan kona majalisar dokoki da masu zanga-zanga suka yi, amma Jean Ping din ya bayyana wa tashar DW takaicin barnata rayukan al’umma da ma dukiyoyi inda ya ce zai kalubalanci shugaba Bongo a gaban kotun hukunta laifukan yaki ta ICC.

Gabun - Präsident Ali Bongo OndimbaShugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba

Shugaba Ali Bongo dai ya dora alhakin duk tarzomar da ta wakana ga madugun ‘yan adawar kasar,kuma ya sha alwashin daukar duk matakan da suka dace domin maido da tsaro dama doka da oda a biranen kasar, to sai ‘yan adawa sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga har sai an sake kididdigar kuri’un zaben domin tantance su.

You may also like