Labaran matan da suka cinnawa kansu wuta saboda “muzgunawar maza”
Labaran matan da suka cinnawa kansu wuta saboda “muzgunawar maza”
Mata a Iraƙi na fuskantar ƙaruwar cin zarafi a gidajen aure da wajen ƴan uwa.
Matsalolin cin zarafi sunƙaruwa da kashi 125 cikin 100 a shekarar 2020 da 2021, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
A yankin Kurdistan na ƙsar, matan da ke samun kansu cikin cin zarafi a gidaje kan ɗauki matakain ƙona kansu da zummar mutuwa a matsayin hanya ɗaya da suke ganin ita ce mafita.
Gwamnatin yankin Kurdistan ta yi ƙoƙarin magance matsalar cin zarafin mata dar muzguna musu da ake yi, amma da yawansu kan kasance cikin haɗari.
An bai wa BBC wata dama da ba a cika samu ba ta shiga manyan asibitocin jinyar masu ƙuna a Kurdistan da ke iraƙi, inda mata da dama suk mutu sakamakon ƙona kansu da suka yi.