Kungiyar manoman Nigeria wato All Farmers Association of Nigeria (AFAN) sunce Adadin yawan manoman da suka koma gonakin su don ci gaba da harkokin su na noma ya kai 18,000 a wannan shekarar. Manoman da suka hakura da gonakin na da noma wa kansu abin da zasu ci har na tsawon shekaru 4 sakamakon rashin zaman lafiya a yankin.
A tattaunawar sa da Kungiyar yan jaridu na kasa wato News Agency of Nigeria (NAN) a maiduguri, Sakataren kungiyar manoman yace manoman Salihu Aliyu yace manoman sun dawo bakin aiki ganin cewa yanzu an samu zaman lafiya ba kamar da ba.
Sannan ya kara da cewa suna tattaunawa da Gwamnatin tarayya da babban bankin Kasa na CBN wajen cewa manoman wadanda yawansu ya kai 18,000 zasu amfana da rancen noman Shinkafa da ake bawa manoma na 4.9billion da CBN tare da hadin gwiwa da gwamnatin tarayya suke bawa manoman shinkafa domin bunkasa noman shinkafa a nigeria.
Tuni manoma 78,000 dake jihar Kebbi suka amfana da rancen kudin daga Babban bankin CBN din. Muma muna son manoman shinkafa na borno su amfana da wannan shirin wato CBN Anchor Borrowers Programme.