Wayar salula ta hannu da kuma na’urar ciro kudi ta ATM wasu abubuwa ne da cigaban kimiya na zamani yazo dasu don saukaka rayuwa tsakanin al’umma, jama’ar Najeriya suma sun bi takwarorinsu na sauran kasashen duniya don yin amafani da wadannan abubuwan cigaban zamanin.
Sai dai kuma wasu batagari na nema su kawo barazana, ga yadda al’ummar jihar kano ke amfani da wadannan na’urori.
Koda a makon da yagabata sai da wani matashi mai suna Muhammad yarasa ransa, bayan da wasu batagari suka caka masa wuka a lokacin da suke kokarin rabashi da wayarsa da kuma kudin da yaciro a na’urar ta ATM a unguwar Kofar Mata dake birnin.
Labari irin wannan da yafaru ga Muhammad, abune da yake nema ya zama ruwan dare a birnin, inda wasu mutanen sukan tsira da rayukansu amma da munanan raunuka.
Mutane da dama dai na alakanta karuwar aikata laifuka a birnin da rashin aikinyi da matasan jihar ke fama dashi, sai dai a tabakin wani mazaunin birnin yace aikata laifuka a jihar nada alaka da yadda shan miyagun kwayoyi ke kara samun gindin zama a jihar.
Alkaluman bayanan da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta fitar na nuni da cewa jihar kano na kan gaba wajen sha da mu’amala da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Abin jira dai a gani shine yadda hukumomi zasu shawo kan al’amarin.