Kwale-kwale ya kife da sojojin Najeriya 


Shugaban kungiyar masu harkokin kasuwanci da jiragen ruwa a jihar Bayelsa Lloyd Sese ya ce al’ummar ta yankin Brass da ke gab da teku su ne suka fara kawo labarin. A cewar rahoton wasu dakarun sojan Najeriya hudu sun lume a ruwa, bayan da jirginsu ya kife alokacin da suke aikin fatattakar ‘yan tawaye a yankin Niger Delta mai arzikin mai, da ke a kudancin kasar. 
Wata majiyar sojan Najeriyar ta bayyana haka a ranar Talatan nan. A cewar majiyar sojan, lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe goma na safe agogon Najeriya a yankin Brass da ke gabar teku a jihar Bayelsa.

A watan da ya gabata dakarun sojan na Najeriya sun kaddamar da wani aikin fatattakar mayakan sakai mai suna “Crocodile Smile” da ke da burin kakkabe ayyukan masu tada kayar baya da fasa bututun mai da ma fashin teku a gabar Tekun Gini.

Shugaban kungiyar masu harkokin kasuwanci da jiragen ruwa a jihar ta Bayelsa Lloyd Sese, ya ce al’ummar ta yankin Brass sun tabbatar da afkuwar lamarin. Haka ma mai magana da yawun sojan na Najeriya Kanal Sani Usman ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP afkuwar lamarin.

You may also like