Kwalera ta barke a Haiti bayan guguwar Matthew


 

Annobar cutar Kwalera ta barke a Haiti a yayin da kasar ke zaman makokin daruruwan mutanen da suka mutu sakamakon bala’in guguwar Matthew. Yanzu haka Kungiyoyin agaji ne ke ci gaba da aikin taimakawa wadanda bala’in guguwar ya shafa.

Guguwar matthew ta kashe kusan mutane 1000 a Haiti, kuma yanzu akalla mutane 15 suka mutu sakamakon annobar cutar Kwallera da ta barke kasar.

Hukumomi a kasar sun yi gargadin cewa cutar za ta ci gaba da yaduwa saboda yadda guguwar Matthew ta haifar da gurbacewar muhalli a kasar.

Kwanaki hudu guguwar ta kwashe tana yin barna a yankin Caribbean, kuma yanzu ta tsallaka zuwa Amurka inda ta hallaka mutane biyar da kuma yin barna a jihohin Florida da Georgia da kudancin Carolina.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like