Kwamacala: Uba Da Ɗansa Sun Yi Wa Ƴarsa Fyaɗe A Jihar Cross Rivers


Wani magidanci da dansa sun shiga hannun hukuma bisa zargin su da yi wa ‘yarsa kuma kanwa ga dan nasa fyade a garin Eshiagurube Boki dake jihar Cross Rivers.

Majiyarmu ta rawaito cewa uba da dan nasa sun kudiri aniyar yi wa ‘ya/kanwar fyade ne a yayin da mahaifiyar yarinyar ta fita unguwa.

Yanzu haka mutumin da dan nasa an mika su wurin jami’an ‘yan sanda.

You may also like