Kwamishina Ya Mutu Lokacin da Suke Gudun Motsa Jiki Tare da Gwamna


simong lalong

Mista Samuel Galadima kwamishinan Gidaje da Raya Birane na jihar Filato ya fadi,ya mutu yau laraba yayin da suke gudun motsa jiki tare da Gwamna Simong Lalong, a Filin Wasa na Rwang Pam dake Jos babban birnin jihar.

Darektan yada labarai na Gwamnan jihar Mista Emanuel Nanle ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, faruwar wannan al’amari.

Mista Nanle yace ” Eh lallai Kwamishina ya fadi lokacin da suke motsa jiki tare da Gwamna, an kuma garzaya da shi asibitin kwararru na jihar Filato inda anan ya mutu”.

You may also like