Andrew Nok, kwamishinan Ilimi,kimiya da Fasaha na Jihar Kaduna ya mutu da safiyar yau Talata yana da shekaru 55.
Shahararren masanin kimiyyar da yayi suna a duniya, ya kwanta a wani asibiti dake Abuja kafin a sallame shi a makon da ya wuce.
Nok wanda shine shugaban tsangayar kimiyya ta jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya kafin gwamna Nasir El-Rufai, ya naɗa shi kwamishinan lafiya na jihar Kaduna a watan Yulin 2015.daga bisani an dauke shi zuwa ma’aikatar Ilimi bayan da gwamna El-Rufai ya yi wa gwamnatinsa garambawul.
A shekarar 2010 an bashi lambar girmamawa ta kasa NNOM a ɓangaren kimiyya.
Marigayin na daga cikin wadanda suka nemi kujerar shugabancin Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a shekarar 2009 duk da cewa shine ya samu kaso 80 na kuri’ar da aka kada Nok ya gaza zama shugaban jami’ar kan batu da ake alakanta shi da addini.