Kwamishinan lura da aikace aikace na jihar Borno ya Rasu. 


Allah yayiwa Kwamishinan lura da aikace aikace na jihar borno  Waziri Imam rasuwa a babban asibitin da yake jami’ar garin na maiduguri,  UNIMAID a yau laraba bayan takaitacciyar rashin lafiya.
Marigayi Waziri imam dai kani ne a wajen dan takarar gwamnan jihar Borno Kashim Imam wanda ya tsaya takarar Gwamna har sau biyu a jam’iyyar PDP.  

Ya zuwa yanzu dai gwannatin jihar borno bata sanar da rasuwar Waziri Imam ba,  amma daga yanzu zuwa ko wanne lokaci ana sa ran sanarwar. 

Muna fatan Allah yaji kansa ya kuma yi masa rahama, da kuma dukkan musulmi da suka rigamu gidan gaskiya. 

You may also like