Kwamishinan yan sandan jihar Abia yace sun gano makamai a gidan Nmandi Kanu


Anthony Ogbizi, kwamishinan yan sandan jihar Abia yace makamai da suka hada da bindiga da kuma bom na fetur aka gano a ranar Lahadi lokacin da suka kai sumame gidan, Nmandi Kanu, shugaban kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra.

Ogbizi ya bayyana ranar Alhamis lokacin da yake ganawa da manema labarai a Umuahia, babban birnin jihar.

Yace an gano kayayyakin yayin wani sumame na hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro dake jihar.

Yace an gudanar da sumamen ne bisa dogaro da bayanan sirri da suka samu dake nuni da cewa yayan kungiyar na cigaba da gudanar da al’amuran su.

Ya kuma ce an kama wani mutum guda da ake zargin da kasancewa mamba a  kungiyar ta IPOB.

Ya ce tawagar jami’an tsaron sun kuma gano nambobin wayar tarho na jami’an tsare-tsaren kungiyar a shiyoyi daban-daban dake kasarnan inda ya kara da cewa za a yi bincike na tsakanin kan tattaunawar da Shugabannin kungiyar suke da juna.

Yace kuskure ne a rika cewa sojoji sun karbi aikin yan sanda yakamata a kalli matakin a matsayin hadin kai na hukumomin biyu wajen maganin matsalar tsaro da ta addabi jihar.
Ogbizi yace ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen gayyato sojoji a kowane lokaci da matsalar tsaro tafi karfin yan sanda.

You may also like