A jiya ne Alhamis Kwamishinar Ilimin Jahar Gombe Hajjia Aisha M.B Ahmad (Magayakin Akko) tasamu lambar yabo Daga EDUCATIONAL CRISIS RESPONSE (ECR) PROJECT a Banquet Hall, Gidan Gwamnatin Garin Bauchi. Wannan Lambar yabo ta same shine bisa Gwazon ta da nuna kokarin ta kan harkar ilimin jahar Gombe wanda ta zamo Zakara kuma abun a yabe ta.
Hajiya Aisha M.B Ahmad (Magayakin Akko) itace kadai tasamu kyautar Lambar Yabo A Komishinonin Arewa Baki daya kaf. Allah yakara daukaka kuma Allah Ya sa sauran abokan aikin ki suyi koyi dake suma su samu lambar yabo kan kokarin kula da harkar ilimin kasa.