Kwamitin binciken da gwamnatin jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta kafa, ya ruwaito cewa mutane 348 ne ‘yan kungiyar Shi’a, sojoji suka kashe biyo bayan wani cece kuce daya shiga tsakanin su a cikin watan Disambar bara.
kwamitin ya jaddada cewa mutane 348 ne na kungiyar ta ‘yan shi’a suka mutu da soja guda sakamakon wannan hatsaniyar.
Suma kungiyoyi kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun fidda kwatankwacin irin wannan rahoton.
Amma rahoton kwamitin na jihar Kaduna ya danganta mafi rinjayen laifin ga kungiyar ta ‘yan Shi’a abinda mai Magana da yawun rundunar sojojin Kasar Kanar Sani Usman ya jaddada.
Sai dai kuma Kanar din yaki yace uffan game game da shawarar da kwamitin na jihar Kaduna ya bayar na cewa a gurfanad da duk wani sojan da aka samu da laifi cikin wannan al’amari na kashe fararen hula har su 348.
Kwamitin yace kungiyar ce ta ingiza ‘ya’yanta suka bijirewa doka.