Kwamitin Hafsan Hafsoshin Najeriya Ya Ceto Dukkan Fasinjojin jirgin Kasan Kaduna Da Aka Yi Garkuwa Dasu
ABUJA, NIGERIA – Kwamitin da Hafsan Hafsoshin Najeriya General L E O Irabor ya hada don ceto sauran fasinjojin jirgin kasan da aka yi garkuwa dasu bayan wani harin ‘yan ta’adda a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022, ya ce ya sami nasarar ceto dukkan mutanen a yau Laraba.

Kwamitin, a ta bakin sakatarensa Farfesa Usman Yusuf a cikin wata sanarwar da ya turawa wakilin Muryar Amurka Alhassan Bala, yace an sami wannan nasarar ne biyo bayan hadin kan sauran jami’an tsaro da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Ina mai farin cikin bayyana wa ‘yan Najeriya da sauran al’ummar duniya cewa a yau Laraba da misalin karfe 4 na yamma, wani kwamiti mai mambobi bakwai da Hafsan Hafsoshin Najeriya ya samar ya sami nasarar ceto dukkan sauran fasinjojin jirgin kasan su 23 da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa dasu,” a cewar sanarwar.

You may also like