Kwamitin Majalisar Dattijai Na Son Ayi Karin Kudin Mai Zuwa N150Kwamitin majalisar dattijai dake kula da aiyuka,ya bada shawarar da akara kudin litar man fetur daga naira 145 zuwa 150 domin samar da kudi ga asusun kula da hanyoyi na kasa. 

Shawarar na zuwa ne shekara guda bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari,ya kara farashin man daga N85 zuwa N145 .

Kara kudin na kunshe ne cikin jerin shawarwarin da kwamitin kula da aiyuka karkashin jagorancin Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya bayar kan kudirin samar da asusun kula da hanyoyi wato (National Road Fund)  a turance. 

Rahoton na cikin abubuwan da majalisar zata tattauna a zamanta na jiya.amma sai aka daga tattaunawa akan batun saboda karancin lokaci. 

Kwamitin dai yabada shawarar karbar N5 akan ko wacce litar mai da aka shigo dashi cikin kasarnan ko kuma aka tace shi a matatun mai na gida. 

Mambobi 12 cikin 15 da kwamitin ya kunsa sun amince da rahoton kwamitin.

You may also like