Kwamitin majalisar wakilai ya bawa rundunar ƴan sanda sa’o’i 48 da su bar harabar ofishin ƙungiyar Peace Corps


Kwamitin majalisar wakilai dake karɓar ƙorafin jama’a ya umarci ƴan sanda kan su fice daga hedikwatar ƙungiyar Peace Corps dake Abuja.

A wani taro da kwamitin ya gudanar ranar Talata, ya nemi ƴan sandan da su fice daga hedikwatar cikin sa’o’i 48.

Taron ya biyo bayan ƙorafin da aka rubutowa majalisar wakilai ta tarayya  kan zargin da ake wa babban sifetan ƴan sanda na ƙasa Ibrahim Idris kan ƙin yarda da ya yi a sake buɗe ofishin  ƙungiyar.

A watan Nuwamba,wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta umarci ƴan sanda da su sake buɗe hedikwatar ƙungiyar da suka rufe tun cikin watan Faburairun shekarar 2017.

Dickson Akoh kwamandan Peace Corps ya ce,Abubakar Malami babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a ya umarci babban sifetan da ya buɗe ofishin amma yaƙi bin umarnin.

You may also like