Kwamitin Sulhu Na APC Ya Bar Baya Da Kura Bayan Mika Rahoto
Shugaban Kwamitin Sanata Abdullahi Adamu ya ce a gaba daya sun samu korafi 47, kuma sun yi bakin kokari wajen sulhun, duk da cewa Kwararru a fannin siyasa sun ce sai fa an ciza an hura.

Kwamitin wanda ya fara aiki a Satumban bara, ya leka wasu jihohi inda akalla ya ba da labarin sulhu tsakanin tsohon gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje da Gwamnan jihar Inuwa Yahaya, duk da haka akwai jihohin da ba a gama warware takaddama ba.

Gabanin mika rahoton, kwamitin ya samu korafin zaman doya da manja tsakanin ‘yan jam’iyyar a jihar Taraba, inda alamu ke nuna sai yanda hali ya yi ga yin sulhun, gabanin babban taron jam’iyyar a ranar 26 ga wanan watan.

Shugaban Kwamitin, Sanata Abdullahi Adamu ya ce rashin kammala aikin ba zai hana gudanar da babban taron ba.

Jigon jam’iyyar APC a Taraba, Alhaji Abdullahi Ade ya ce su na fatan jam’iyyar ta tabuka abun kirki a shekara 2023.

To sai dai ga masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jamiár Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk yana ganin ba lallai ba ne sulhun yayi tasirin da ake fata fiye da a ciza a hura.

Rashin gudanar da sulhu ko biris da korafin ‘yan jam’iyya ya jawo rasa Kujerar tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole da ya zama wajibi a gareshi ya janye kara daga kotu don sa bakin Shugaba Buhari a dambarwar.

You may also like