Kwamitin Tallafi Na Shugaban Najeriya Na Arewa Maso Gabas YaYi Taro Da KwararruKwamitin tallafawa al’ummar arewa maso gabas da ke ƙarƙashin Janar Theophilus Danjuma ya gana da kwararru don tara karin bayanai hanyoyin shawo dukkan kalubalen da al’ummar yankin ke fuskanta daidai lokacin da su ke farfadowa daga illar Boko Haram.

Taron wanda ya gudana a Hotel din Custodian dake garin Gombe a jihar Gombe da ke tsakiyar jihohi 6 na yankin, ya samu halartar farfesa Jibrin Ibrahim wanda ya nanata batun iyaye su rika cusa tarbiyya a zukatan yara don hana su kangarewa in sun girma.

Farfesa Ibrahim ya kara da cewa ya zama wajibi al’ummar yankin su kara jajircewa da kula da duk bakin da kan shigo yankin su don tantance na gari da mugu.

Hakanan Farfesan ya ba da shawarar gina gidaje a waje daya maimakon yadda kauyuka su ke da gidaje da ke jefe da tazara da juna da hakan kan ba wa ‘yan ta’adda damar dauki daddaya ga jama’a.

Mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Tumsa ya yi alwashin ci gaba da aiki tukuru don tallafawa al’ummar yankin musamman wadanda su ka rasa matsugunan su, su koma garuruwan su na asali.

Tumsa ya ce kwamitin zai bullo da hanyoyin yaki da talauci don yankin na kan gaba wajen fama da kuncin talauci a Najeriya.

Sauran wadanda su ka yi sharhi sun ba da misalin tasirin sanya idon al’umma da ya tallafa wajen dakile illar ‘yan Boko Haram a garin Biu da kuma jihar Jigawa duk da su na yankunan da ‘yan ta’addan su ka yi wa kaka-gida.

You may also like