Kwankwasiyya Sun Nemi Gafarar Kanawa bisa Kawo Ganduje Da sukai***Mun Tuba Ku Yafe Mana Kuskuren Kawo Ganduje Da Muka Yi.

Shugaban kungiyar hannun karba hannun rikewa Sharu Umar Gwammaja ya nemi gafarar Kanawa sakamakon tsayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin jihar Kano. Gwammaja yayi wannan furuci ne a yayin bikin cikar zagayowar ranar haihuwar tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso shekaru 60.

” A baya mun yi wa Ganduje tayin Naira Miliyan Ɗaya domin cire jar hula, amma ya ki amincewa. Don haka yanzu mun ba shi awa 48 ya cire jar hula ko mu maka shi a kotu. Tun da dai ya sauka daga kan akidar Kwankwasiyya. Kuma muna neman afuwar Kanawa na kawo Ganduje da muka yi. Mun yi nadamar wannan aiki namu, amma a yayin zabe na gaba za mu sauya shi da wani. Muna fatan za a karbi tuban mu”.

You may also like