Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, rahotannin dake ishe mu ta karkashin kasa na nuni da cewar Madugun Jam’iyyar APC na kasa Bola Tinubu da Madugun darikar Kwankwasiyya sun yi nisa wajen kulle kulle don kafa wata sabuwa kuma kakkarfar Jam’iyya wadda za ta hado gamayyar Jam’iyyu da ake zaton zasu yi mata rijista da sunan (Mega Party) kafin 2018.
Ana dai hasashen gwamnoni da dama, Sanatoci, ‘Yan Majalisun Tarayya da na jihohi dama wasu gaggan ‘yan siyasa daga dukkan sassan kasar nan kuma daga mabambantan jam’iyyu ne zasu kasance a cikin wannan gamayya. Ko a kwanakin baya Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda Wamakko domin tattauna wasu Muhimman bayanai da suka shafi siyasa.