Kwankwaso Ya Dage Da Batun Zuwansa Kano


Tsohon gwamanan jihar Kano, kuma Sanata Mai wakiltar Kano ta tsakiya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya dage batun zuwan sa jihar Kano a gobe Talata.

A yayin da yake magana ta bakin tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Rabi’u Bichi, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya dage batun zuwan ne bayan wasu shawarwari da ya samu daga wasu masu fada a ji daga sassa daban daban na kasar nan.

You may also like