Kwankwaso Ya Zabi Fasto Bishop Isaac Idahosa A Matsayin Mataimakinsa A Zaben 2023WASHINGTON, D.C – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso ya zabi Fasto Bishop Isaac Idahosa a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.

Presidential candidate of the New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso

Presidential candidate of the New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis da cewa “Mataimakin Shugaban Kasarmu Fasto Bishop Isaac Idahosa daga jihar Edo.”

Pastor Bishop Isaac Idahosa

Pastor Bishop Isaac Idahosa

Bishop Idahosa, wanda ya fito daga jihar Edo shi ne babban Fasto na God First Ministry, da aka fi sani da Illumination Assembly.

Cocin na da hedikwata ne a Lekki, jihar Legas.

You may also like