Kwastam Sun Kama Bindigogi 440 Da Aka Shigo Dasu Daga Kasar Turkiya Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wato (kwastam), tace ta kama wata kwantena  makare da bindigogi a tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island dake Lagos,Kwantenar dai ta fito ne daga kasar Turkiya.

Monday Obue,shugaban kwastam mai kula da Tin Can Island ya bayyana haka ga manema labarai inda yace an boye bindigogin ta hanyar yin karya wajen bayyana abin da Kwantenar ke dauke dashi.

Yace Kwantenar tana dauke da bindigogi 440 da kuma harsashi mai yawan gaske.

Yace hukumar ta kaddamar da bincike domin gano wanda ya shigo dasu.

Ya zuwa yanzu dai  hukumar ta kama mutum daya dake da hannu a shigo da makaman.

Hakan na zuwa ne watanni  kadan bayan da hukumar, ta kama wasu makamai a jihar ta Legas.  

You may also like