Kwazon Kananan Hukumomi Zai Rage Wa Jihohi Nauyin Jama’a —Gwamnan Bauchi


 

bauchi-gov

Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar na Jihar Bauchi ya ce kananan hukumomi su ne jagaba wajen yaki da talauci da bayar da gudunmawa ga bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya kuma bayyana cewa idan aka bayar da iko ga kananan hukomomin wajen magance matsalolin da suka yi wa al’umma katutu kamar su yaki da talauci, samar da kayan more rayuwa, tabbas gwamnatocin jihohi da ta tarayya za su samu saukin aiki da bullo da hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi kasar na.

Gwamnan Jihar Bauchi ya bayyana hakan ne a sa’ilin da yake ganawa da shugabanin riko na kananan hukumomi 20 Jihar Bauchi. Ya ci gaba da cewa tilas babu makawa sai an samar da tsari mai kyau kafin a iya shawo kan damuwowin da suka yi katutu ga al’umma.
Gwamna Abubakar ya  zargi gwamnatotin da suka shude da maida kananan hukumominsu wurin hira inda ya yi nuni da cewa da zaran wata ya kare, za su nemi albashi ba tare da gudanar da ayyukan da ke kawunansu ba.

Sai ya bukaci sabbin shuwagabanin kananan hukumomin da su tabbatar sun samar da hanyoyin kudaden shiga a yankunansu, kana ya tunatar da su game da daukan rantsuwa na kama aiki da suka yi, inda ya ce akwai bukatar su zage damtse wajen gudanar da ayyukansu.
Da yake jawabi a madadin shugabanin, mai rikon mukamin shugaban Karamar Hukumar Bauchi, Adamu Abubakar ya tabbatar wa gwamnan cewa ya zuwa yanzu shuwagabanin sun mai da hankalinsu ne wajen nemo hanyoyin warware matsalolin da suke addabar kananan hukumomin da kuma gudanar da ayyukan da aka tura su su yi inda ya bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen yin abubuwan da suka kamata a dan lokacin da aka ba su.

You may also like