
Asalin hoton, Getty Images
Za a ci gaba da wasannin La Liga karawar mako na 27, inda za a fara wasa tun daga ranar Juma’a.
Real Mallorca ce za ta karbi bakuncin Osasuna – Osasuna tana ta taran teburi mai maki 34, ita kuwa Mallorca maki 32 ne da ita ta 11 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ranar Lahadi Real Betis za ta ziyarci Atletico Madrid, kungiyoyin da ke fatan zama cikin ‘yan hudun farko, suna son tsawaita wasa ba tare da an doke su ba a lik.
Bayan fara kakar bana da cin karo da kalubale, Diego Simone ya doke Valencia 3-0 kafin ayi hutu, kenan Atletico ta yi karawa 10 a jere ba tare da rashin nasara ba.
Akwai karin bayanai………