Labarai A Takaice  Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu abinda ya sauya dangane da abinda ya shafi dangantakar ta da Nijeriya bayan wani samame da sojin kasar suka kai sansanin ta da ke Maiduguri.

– Hukumomin Nijeriya sun kama wasu ‘yan kasar China 8 da ake zargi da hakar ma’adinai a Jihar Plateau ba tare da izini ba.

– A Nijeriya matsalar zazzabin cizon sauro a jihar Kano da ke arewacin kasar na neman zama wata babbar barazana, kasancewar zazzabin ya fara karade lungu da sako na jihar.

– Jagoran ‘yan adawar Kenya Raila Odinga na nazarin matakin da zai dauka nan gaba bayan ya yi watsi da sakamakon zaben shugabancin kasar da ya ce, an tafka makudi a cikinsa.

– Fadar gwamnatin Amurka ta jaddada cewa, shugaban kasar Donald Trump, ya yi alla-wadai ga dukkanin bangarorin da ke da hannu a zanga-zangar wariyar launin fata da ta yi sanadiyar mutuwar wata matashiya a birnin Charlottesville na jihar Virginia.

– Majalisar Kasar Iran ta amince da wata doka da zata takaita aiwatar da hukuncin kisan kai, kan mutanen da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar.

– Soyayyar da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ke samu daga al’ummar kasar na disashewa a dai-dai lokacin da shugaban ke shirin cika kwananki 100 a karagar mulki.

– Iran ta ce tana iya ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da wasu kasashen Yammacin duniya muddin kasar Amurka ta ci gaba da sanya mata takunkumi.

– Hukumar kwallon kafar Spain ta sanar da dakatar da Cristiano Ronaldo daga buga wasanni 5 saboda samun sa da laifin ture alkalin wasa da yayi a karawar da Real Madrid tayi da Barcelona.

You may also like