Labarai A Takaice A Najeriya mukaddashin shugaban Hukumar da ke yaki da rashawa ta kasar , EFCC, Ibrahim Magu ya ce babu abinda zai razana su dangane da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai ofishin su da ke Abuja. 

– Kungiyar dake kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, tace hanyoyin da za’a bi domin magance matsalolin da yan gudun hijira ke fuskanta shine a maida su garuruwan su, da aka tabbata an samu zaman lafiya.

– A Najeriya dukiya ta miliyoyin naira da dabbobi ne suka salwanta a jihar Adamawa arewa maso gabashin kasar sakamakon ambaliyan ruwa da aka yi a yankin Shelleng dake kudancin jihar.

– Kafar sadarwar WhatsApp na shirin fitar da wata sabuwar hanya da masu amfani da manhajar za su iya aikawa junansu kudi ta hanyar aika sakon karta kwana.

– A jiya alhamis ake saran kotun hukunta manyan laifufuka da ke birnin Hague ta bayyana hukunci kan biyan diyyar wuraren tarihin da aka lalata a Timbuktu da ke kasar Mali.

– Hadakar kungiyoyin matan Nijar ta bukaci mahukumtan kasar su gaggauta ceto mata 33 da Boko Haram ke garkuwa da su da wasu shida da suka bace wajen makonni shida da suka gabata. 

– Shugban kasar Zimbabwe Mr Robert Mugabe, ya isa kasar Afirka ta Kudu, domin ya taimakawa uwargidansa Grace, wadda ta mika kanta ga jami’an tsaron kasar a sakamakon zarginta da lakadawa wata matashiya data kama da ‘ya’yanta a wani dakin Otal duka da wayar wuta.

– Shugaban Kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-In ya ce babu wani yakin da za a gwabza a Yankin su, domin kasar sa ke da hurumin bada umurni ga sojojin Amurka na mayar da martini kan duk wata takala daga koriya ta Arewa.

– Wani Binciken masana kiwon lafiya ya ce wasu kananan cututuka da ke kama huhu sun hallaka mutane sama da miliyan uku da rabi a shekarar 2015.
-Buhari Ya Cika Kwana 100 a kasar landan

You may also like