Labarai A Takaice 


 
Shugaban Angola Jose Eduardo Dos Santos da ya dare kan karagar mulki tun shekarar 1979, ba zai tsaya takara ba a zaben gama-gari da za a gudanar a gobe Laraba.

– A Saudi Arabia tsananin zafi da ake fama da shi a kasar na tilasta wa wasu maniyata aikin hajji zama a masaukinsu don kare kansu daga kamuwa da cutukan da zafin ke haifarwa, masana ilimin taurari kasar na hasashen cewa,  tsananin zafin ranar na iya kai wa har maki 65 na ma’aunin selshiyos nan da watan gobe.

– Wasu sojin ruwan Amurka guda goma sun bace wasu biyar kuma suka jikkata bayan da jirgin ruwan sojin Amurka mai suna “USS John S. McCaine” yayi karo da wani jirgin jigilar kayan ‘yan kasuwa a gabashin Singapore kusa da tekun Malacca.

– Jami’an ‘Yan sandan Spain sun halaka Younes Abouyaaqoub da ake zargi da kai harin Bercelona da ya kashe mutane 16 tare da jikkata sama da 100, akasarinsu ‘yan kasashen ketare.

– Fadar Shugaban Faransa ta ce zata bai wa uwargidan shugaba Emmanuel Macron aikin yi domin wakiltar kasar sai dai bashi da albashi ko kuma kasafin kudi na sa.

– Masana kimiyya da suka kware kan fasahar kera mutun-mutumi da wasu suka fi sani da sakandami, sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta haramta kera sakandaman da za a iya amfani da su wajen kisan jama’a da kuma a fagen yaki.

– Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin girke karin sojoji 4,000 a Afghanistan sabanin shirin sa na janye dakarun Amurka daga kasar, yayin da ya zargi Pakistan da bai wa mayakan Taliban mafaka a cikin kasar ta.

You may also like