Labarai A Takaice A Najeriya yanzu haka Jamaa sun fara kokawa game da farashin ragunan layya, da yawan mutane na cewa ko baya ga tashin farashin raguna haka kuma kudi sunyi wahalar samu.Hatta suma masu sayar da ragunan sun koka akan rashin kasuwa, Sai dai wasu Rahotannin kuma sun nuna cewa farashin ragunan faduwa yayi a kasuwanni ba wai hawa yayi ba. 

– A Najeriya an bullo da tsarin ciyar da alhazan kasar, sabanin yadda ake barin Alhaji ya nemi abinci da kansa. Yanzu ana iya cewa jigilar  Alhazan Najeriya an sha karfin sa  domin yanzu makonni 4 kenan da fara wannan aiki.

– Majalisar Dinkin Duniya ta koka bisa yadda ta ce yawan fararen hula, da rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya raba da muhallansu ya ninka cikin watanni 6.

– Kwamishinan kungiyar tarayyar turai, ya ce Brussels za ta dauki matakin katse tallafin da take baiwa kasashen da bakin haure ke fitowa daga nahiyar Afirka da Asiya, tare da saka ka’idoji kan harkokin kasuwanci, da ba da takardun visa, domin a tilasta musu karbar bakin hauren da ba su sami mafaka ba.

– A Faransa sakamakon wata sabuwar kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Faransa ta nuna cewa yawan ‘yan kasar da suke nuna rashin gamsuwa da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ya karu daga watan Yuli zuwa yau.

– Gwamnatin Venezuela ta kaddamar da atasayen sojin na tsawon kwanaki biyu a fadin kasar, wani mataki na tauna tsakuwa don aya taji tsoro, bayanda shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar yin amfani da karfin soja wajen kawo karshen shugabancin Nicolas Maduro.

– Gwamnatin Venezuela ta kaddamar da atasayen sojin na tsawon kwanaki biyu a fadin kasar, wani mataki na tauna tsakuwa don aya taji tsoro, bayanda shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar yin amfani da karfin soja wajen kawo karshen shugabancin Nicolas Maduro.

– A Indiya masu zanga-zanga magoya bayan Ram Rahim Singh, sun fara tafiya gidajensu domin kawo karshen jan daga da sojoji.

– Ana ci gaba da samun rashin goyon baya ga hukuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na yiwa tsohon babban jami’in ‘yan sandan jihar Arizona afuwa, bayan da aka same shi da laifin nuna wariya.

– China ta fara aiwatar da matakan takunkumin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince a kakabawa Korea ta Arewa bayan da Korean ta yi gwajin makamai masu linzami.

– Magoya bayan malamin addibi a kasar India, Ram Rahim Singh sun janye daga arrangamar da suke cigaba da yi da jami’an tsaron kasar, wanda suka fara a ranar Juma’ar da ta gabata.

You may also like