Labarai A Takaice – Gwamnatin Najeriya ta amince da bada kwangilar gina tashar samar da wutar lantarkin Mambila akan kudi sama da Dala biliyan 5 da rabi domin samar da megawatt 3,050 a Gembu dake Jihar Taraba.

– Shugaban Hukumar EFCC a Najeriya Ibrahim Magu ya ce sun yi nasarar karbo sama da naira biliyan 409 da Dala miliyan 69 a cikin shekara guda duk da matsalolin da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu.

– Gwamnatin Birtaniya ta yi alkawalin ba Najeriya taimakon Fam miliyan 200 a cikin shekaru 5 masu zuwa domin magance matsalar da Boko Haram ta haifar.

– Gwamnatin Kasar Nijar ta ce mutane 44 suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu tsakanin watan Yuni zuwa yau, yayin da sama da 70,000 suka rasa muhallinsu.

– Sama da Mahajjata miliyan 2 daga sassan duniya da ke aikin hajji a Saudiya sukai tsayuwar Arfah a jiya Alhamis, wanda shi ne rukuni mai girma cikin rukunan aikin hajji.

– Hukumomin Houston a Amurka sun kafa dokar hana fitar dare domin magance matsalar satar kayan jama’a da ake samu sakamakon ambaliyar da ta mamaye birnin yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan agaji.

– An Kammala Hada Hadar cinikayyar yan kwallon duniya a daren jiya. 

You may also like