Labarai A Takaice – Wani rikicin siyasa da ya barke tsakanin magoya bayan Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi sanadin jikkata mutane 20 ciki harda manyan tsofaffin Jami’an gwamnatin jihar.

– Wata cuta da ake tunanin ta amai da gudawa ce, ta yi sanadin mutuwar mutane 14 a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

– Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taro yau Talata domin amincewa da matakan sanyawa bangarorin dake karya yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Mali takunkumi.

– Hukumar Zaben kasar Kenya ta sanya ranar 17 ga watan Oktoba a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasar bayan kotun koli ta soke zaben Uhuru Kenyatta a makon jiya.

– Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika, Alpaha Conde ya bayyana cewa, hukuncin da Kotun Kolin Kenya ta yanke na soke zaben Uhuru Kenyatta, wata daraja ce ga nahiyar Afrika.

– Amurka ta ce shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya kusa kure hakurinta duk da cewa ba wai Amurkan na son tsunduma cikin yaki ba ne, kamar yadda Jakadiyar kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta fada.

– Ministar harkokin kasar waje ta Indonesia, Retno Marsudi, tana ziyara a kasar Myanmar domin ganawa da jagabar al’ummar kasar Aung San Su Kyi, da kwamandan rundunar sojan kasar, da kuma  babban mai  baiwa  shugaban kasar  shawara a harkokin tsaro.

You may also like