Labarai A Takaice – 21/5/2017  ‘Yan matan makarantar Chibok tamanin da biyu (82) da ‘yan kungiyar Boko Haram  suka yi musanyarsu da wadansu mayakan ta sun gana da iyayensu a babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi ta kukan murna saduwa da iyayensu, a karon farko tun bayan sako su.
– A karon farko wata kotu a Nijeriya ta mallakawa Gwamnatin kasar miliyoyin Naira da hukumar EFCC ta kama a Lagos, hukuncin da ake ganin ya kama hanyar mallakawa Gwamnati duka wasu kudade da hukumar EFCC za ta kama a nan gaba muddin dai aka kasa samun wanda ya mallaki kudaden da EFCC ke kamawa.
– Kayan masarufi sun fara tashin goron zabi a kasuwani, a birnin Maiduguri a daidai wannan lokacin da al’ummar musulmi ke shirin fara azumin watan Ramadan.
– Shugaban Sudan Omar Hassan al Bashir da kotun duniya ta ICC ke tuhuma da aikata laifukan yaki, ya sanar da kauracewa taron shugabannin kasashen Musulmi da za a gudanar a Saudiya tare da shugaban Amurka Donald Trump.
– Amurka da Saudiya sun kulla ‘yarjejeniya cinikin makamai da kudin su ya kai dalar Amurka biliyan 110 a ziyarar farko da Shugaban Amurka Donald Trump ya kai kasar.
– Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Juma’a da kashi 57 cikin 100 na yawan kuri’un da mutane fiye da miliyan 40 suka kada.
– Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan fararen hula da ke gujewa yaki a Mosul na Iraqi na neman su gagari kundila, matakin da ya jefa kungiyoyin agaji cikin mawuyacin hali kan hidima da bukatun dubban mutanen.
– Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ziyararsa ta farko a yankin Afrika tun bayan darewa kan karagar mulki, in da zai yada zango a Mali a yau Juma’a domin ganawa da sojojin Faransa da ke yaki da ‘yan ta’adda.
– Qatar ta sanar kammala aikin ginin daya daga cikin filayen wasannin kwallon kafa domin wasannin gasar cin kofin duniya da za ta karbi bakunci a 2022.

You may also like