Labarai A Takaice – Hukumar Kwastam a Najeriya ta sanar da kama wasu bindigogi 1,100 da aka shiga da su kasar ba tare da izini ba. Shugaban hukumar Kanar Hameed Ali ya ce anyi safarar makaman ne daga kasar Turkiya.

– Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin bil adama da aka ce sojojin kasar na aikatawa ya fara aiki.

– Kungiyoyin Fararen hula a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun gabatar da abin da suka kira ranakun gudanar da zabubukan kasar inda suka bukaci hukumar zabe ta amince da su.

– Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya kaddamar da cibiyar rundunar sojin kasashe 5 da zasu yi yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

– Wani Binciken masana kiwon lafiya ya bayyana cewar shakar hayakin taba na sauya hanyoyin jinin huhu, abinda ke taimakawa wajen haifar da cutar sankara ko kansa.

– Kungiyoyin Kwadago a Faransa na gudanar da wani yajin aiki da kuma zanga-zanga domin nuna adawar su da shirin shugaban kasar Emmanuel Macron na sauya dokar kwadago.

– Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar da wani taron gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a Myanmar bayan da hukumar kare hakkin Bil Adama ta yi zargin kisan kare dangi.

– Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da Karin wasu takunkumai masu tsauri kan kasar Koriya ta Arewa wadanda suka hada da hana ta fitar da kayan da masakun ta ke sarrafawa da kuma takaita sayar mata da albarkatun mai saboda gwajin makamin da ta yi.

– Shugaban mabiya addinin Buddha na Tibet, Dali Lama ya yi kira ga jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi da ta kokar ta ta ga cewa an kawo karshen tashin hankalin da ke addabar ‘yan jinsin Rohingya na kasarta.

– Mazauna tsibirin  da ke kudancin Florida inda  mahaukaciyar guguwar nan ta Irma ta yi  wa mummunar illa, yanzu  haka ba  za su  iya  dawo  wa  gidajen  su ba har  na tsawon makonni, kamar yadda  fadar  shugaban Amurka ta White  House  ta  fada jiya Litinin.

– Mai horar da Manchester United Jose Mourinho, ya ce kungiyar ta gaza kare martabar kwarewar da aka santa a kai, a karkashin jagorancin David Moyes da kuma Louis Van Gaal, tun bayan ritayar, Sir Alex Ferguson a shekarar 2013.

You may also like