Labarai A Takaice  Shugaba Muhammad Buhari a karon farko tun dawowarsa daga jinya a London ya kaddamar da wani katafaren kamfanin kyankyashe ‘yan tsaki da sarafa waken soya da masara a jihar Kaduna.

– Rikicin da ake yi kan fafatukar awaren ‘yan kabilar Igbo da Nnamdi Kanu ke jagoranta ya dau wani sabon salo, bayan da wasu magoya bayan Kanun su ka shiga far ma mutane tun bayan da yinkurinsu na yin arangama da sojoji ya ci tura.

– Gwamnatin Jihar Abia da ke yankin kudancin Najeriya ta kafa dokar hana fitar dare har tsawon kwanaki uku sakamakon arangamar da aka yi tsakanin masu fafutukar kafa kasar Biafra da sojojin gwamnati.

– Hukumar da ke kula da samar da makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, IAEA, ta mayar da martani kan caccakar da Amurka ta yi mata dangane da yarjejeniyar Nukiliyar Iran.

– Jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta soke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya da za a fara gudanarwa a makon gobe saboda rikicin ‘yan kabilar Rohingya.

– Kotun kolin Amurka ta bai wa shugaba Donald Trump damar aiwatar da dokarsa ta hana baki shiga cikin kasar daga kasashen duniya.

– Gwamnatin Faransa ta bayyana cewa, jami’an tsaron kasar sun yi nasarar dakile hare-haren ta’addanci har 12 da aka yi shirin kai wa kasar a cikin wannan shekarar.

You may also like