– Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta kammala jigilar ‘yan kasar daga Saudiya da suka yi aikin hajjin bana.
– Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi al’ummar kasar sabbin alkawari yayin da yake musu jawabi a ranar bikin cikar kasar shekara 57 da samun ‘yancin kai.
– Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi bikin cika shekaru 57 da samun ‘yancin kan Najeriya tare da rundunar Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram a garin Maiduguri na Jihar Borno.
– A kasar Kamaru Jami’an tsaro kasar sun kashe mutum bakwai yayin da suke zanga-zangar neman ballewar yankin da ke magana da Turancin Inglishi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
– Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu yayin da sama da 100 suka jikkata bayan wani mutun dauke da bindiga ya bude wuta a wani gidan rawa da ke birnin Las Vegas na Amurka.
– Shugaban Amurka Donald Trump ya fada wa sakataren harkokin wajensa cewa ya daina ɓata lokacinsa wajen tattaunawa da Koriya Ta Arewa game da shirinta na nukiliya.
– Shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont ya ce, yankin ya amince da shirin ballewa daga kasar Spain bayan kashi 90 cikin 100 na masu kada kuri’a a zaben raba gardama sun goyi bayan matakin ballewar.
– Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin da wani mutum ya kaddamar da wuka a birnin Marseille na Faransa, in da ya kashe mata 2 kafin daga bisani sojoji su samu nasarar harbe shi har lahira.
– Daruruwan mabiya Shi’a sun gudanar gangami a birnin Karbala na Iraqi kamar yadda suka saba duk shekara domin gudanar da ibada ta jimamin kisan jikokin Manzon Allah (S.A.W).