Labarai A Takaice – Gamayyar kungiyar kamfanonin Najeriya ta zargi babban bankin CBN na Najeriya da yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta hanyar saka masu gadar zare wajen samun sayen kudaden kasashen waje.

– Gwamnatin Najeriya ta ce babu dalilin bukatar dawo da tsohuwar ministan man fetur Diezani Allison Madukwe daga Burtaniya domin fuskantar shari’a a Kasar. 

– An tsinto gawarwaki 16 cikin mutum sama da 50 da kwale-kwale ya nitse da su ranar talatan da ta gabata a garin Yawuri na jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya.

– Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari kan tawagar sojojin Amurka da Nijar da ke aiki kusa da iyakar Mali inda suka kashe sojoji da dama.

– ‘Yan ta’addan kasar Mali dake yawan kutsawa kasar Nijar sun ketara cikin kasar jiya Laraba a yankin Tilaberi inda suka kashe sojojin Nijar da na Amurka yayinda suke sintiri.

– Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci hukumomin Kasar Kamaru su gudanar da bincike akan yadda jami’an tsaro suka kai munanan hare hare kan masu zanga zanga.

– Majalisar Dattawn Amurka zata cigaba da binciken zargin da ake yiwa Rasha cewa ta yiwa zaben Amurka na shekarar 2016 shishshigi da nufin karkata tunanen masu zabe. 

– Wani rahotan bincike ya bayyana cewar kashi 40 na mutanen Amurka da ke fama da cutar sankara ko kuma kansa na da nasaba ne da kibar da ta wuce kima.

– Kasashen Afrika na fuskantar fushin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA sakamakon saba dokokin hukumar a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

You may also like