Labarai A Takaice – A Najeriya  ziyarar da ministar harkokin mata, Hajiya Jummai Alhassan, ta kai hedikwatar jam’iyyar PDP a Abuja ta janyo cece-kucen siyasa, duk kuwa da cewa ba kawai tsohuwar jam’iyyarta ta PDP ta kaiwa irin wannan ziyarar ba; har ma da jam’iyyarta ta yanzu, APC, da ma hukumar zabe ta kasa (INEC).

– A Najeriya yayin da kowane bangare na kasar ke fama da karancin kudi ko kuma rashinsa kwata-kwata, shawarar da Ministar kudin Najeriya ta bayar cewa kowa a rinka biyan haraji har ma da mabarata ta janyo takaddama.

– An gano bakin haure 23 ciki har da yaro dan shekaru 7 a Nijar bayan da masu yi masu jagora suka yi watsi da su a cikin dajin hamada da ke arewacin kasar.Wasu daga cikin mutanen da aka gano ‘yan asalin kasar Senegal da kuma Gambia ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Libya daga Agadez.

– Mahukunta a jihar Maradi a Jamhuriyyar Nijar sun dauki sabbin matakai domin kare rayukan yara kanana, lura da yadda suke fadawa rijiya a lokacin da suke kokarin dibar ruwa. An kiyasta cewa yara 12 ne suka rasa rayukansu a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan a jihar lokacin da suke je rijiya domin janyo ruwa.

– Faransa ta sha gaban Amurka da Birtaniya a Karfin fada aji ta fuskar diflomasiya ba tare da nuna karfin soji ba, kamar yadda wani sakamakon bincike ya nuna. binciken ya ce shugaba Emanuel Macron ne ya daga darajar Faransa kan sauran manyan kasashen.

– Gasar matasa ta kera mutun-mutumi ta duniya a kasar Amurka, na kara jan hankali, musamman yadda ‘yan mata ke taka muhimmiyar rawa. A ‘yan kwanakin bayane gwamnatin kasar Amurka, ta hana wasu ‘yan mata masu hazaka daga kasar Afghanistan takardun shiga kasar ‘Visa’ har sau biyu.

– Fadar Shugaban Amurka tace sau biyu shugaba Donald Trump ya gana da shugaba Vladimir Putin na Rasha a wajen taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki da akayi a Hamburg dake Jamus.

– Hukumomin Kasar Philippines sun ce an raunana masu tsaron shugaban kasar Rodrigo Duterte lokacin da aka budewa tawagar motocin su wuta kwana guda bayan yan tawayen kasar sun sanar da shirin kaddamar da sabbin hare hare.

– Pierre de Villiers Shugaban rundunar sojan kasar Faransa ya yi murabus, Shugaban kasar Emmanuel Macron nan take ya sanar da shiga tattaunawa da Janar Francois Lecontre da ake sa ran zai rike wannan matsayi.

You may also like