Labarai A Takaice  Kwamandan rundunar sojojin Najeriya dake Maiduguri, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya tabbatar da hallaka wasu mayakan Boko Haram 15 sakamakon yunkurin da suka yi na kai hari kan sojojin Najeriya dake garin Gwoza a jihar Borno.

– Rundunar tsaro ta jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane uku yayinda wasu suka samu raunuka a wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Were cikin karamar hukumar Barkin Ladi.

– A garin Konni dake kan iyakar Jumhuriyar Nijar da Najeriya ne aka cafke mugayen kwayoyi da kudinsu suka haya sefa miliyan talatin da bakwai, abinda mahukumtan Nijar suka ce ba shi ne karo na farko ba da kwayoyi ke shigo musu daga Najeriya.

– Hukumar Zabe a kasar Liberia ta jinkirta gabatar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi domin bayyana wanda zai maye gurbin Ellen John Sirleaf.

– ‘Yan Adawa a kasar Togo sun ki janye shirinsu na gudanar da zanga-zanga guda biyu a makon gobe duk da haramcin da gwamnatin kasar ta sanar.

– Kungiyar Kasashen Turai ta ce mutane sama da 500,000 ke mutuwa a fadin Turai kowacce shekara sakamakon shakar gurbatacciyar iska duk da kokarin da hukumomi ke yi na magance gurbacewar muhalli.

– Mawakin Amurka Eminem ya caccaki Donald Trump a cikin wani bidiyonsa inda ya kira shugaban babban mai nuna wariyar launin fata tare da danganta shi a matsayin Kamikaze. Kuna iya kallon bidiyon mawakin.

– Fitaccen mai shirye fina-finai a masana’antar Hollywood ta Amurka, Harvey Weinstein na ci gaba da shan suka sakamakon zarginsa da wasu mata suka yi, in da suka bayyana cewa sai ya yi lalata da su kafin ba su damar haskawa a fina-finai.

– Neymar na Brazil ya fito ya bayyana farin cikinsa akan nasarar da Argentina ta samu na zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a badi a Rasha.

You may also like