Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, sun yi alkawarin kara inganta huldar tsaro da tattalin arziki tsakanin kasashensu bayan sun tattauna a Ankara.
– A jihar Borno Yara daliban Firamare na gujewa makarantu a sakamakon jita-jita da ta bazu a gari cewa za a yi alluran rigakafi a tsakiyar kai da kuma cibi matakin da har ya sa iyaye ke kwashe ‘yayansu a makarantun na Firamare. Sai dai hukumomin jihar sun karyata jita-jitar.
– Shugabannin Tarayyar Turai sun yi alkawarin ba da karin kudade a jiya Alhamis, domin taimakawa Italiya da Libya wajen dakile kwararar bakin haure daga arewacin Afirka dake kokarin isa nahiyar ta turai.
– Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya tabbatar cewa kasar na binciken musabbabin mutuwar sojojinta hudu a jamhuriyar Nijar da mayakan IS suka yiwa kwantan bauna.
– A kasar Togo akalla mutane hudu aka kashe a arrangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar neman kawo karshen mulki Shugaba Faure Gnassingbe.
– Madugun yan adawar Kenya ya ki shiga zaben da kotun kolin kasar ta ce a sake yi ya sa jam’iyyar dake mulkin kasar ta Kenya kiran kotun ta hukumta Raila Odinga.
– Kungiyar International Crisis Group da ke nazari kan rikice rikice a duniya ta ce abu ne mai yiyuwa mazauna yankunan da ke magana da Turancin Ingilishi a kasar Kamaru su fara yin amfani da makamai a gwagwarmayar da suke yi.