Labarai A Takaice 


Akalla kananan yara 11 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da tarin Shika a kauyen Kan-kwana a karamar hukumar Kiru a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya. Jami’in yada labaran karamar hukumar Malam Rabi’u Khalil ya ce wasu yara akalla su 40 na karbar magani.

– Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da ficewar sojojin Chadi da ke yaki da kungiyar Boko Haram a Yankin Diffa, tare da cewa sun janye ne kada kadan a watanni shida.

– Kakakin hukumar yaki da fataucin mutane NAPTIP. Mr. Josiah Emeron yace, bisa yadda ake kwarmata masu bayyanai da kuma irin binciken kwakwaf da suke yi, sun sami nasssarar damke akalla mutane dubu shida, dake da hannu wajan safarar mutane.

– Wani sabon bincike yace abubuwa da suka fi kashe mutane kuma suke haddasa mutuwa farab daya sune yaki, ta’addanci, bala’oi daga Allah, da tabar sigari da kuma cututtuka.

– An kashe akalla dakarun tsaron Masar 53 a wani artabu cikin Saharar Kudancin kasar.

– Hukumomin kare hakkin Dan’adam sun yi Alla-wadai da nada Shugaba Robert Mugabe a matsayin farin jakadan Hukumar Majalisar Dinkin Duniya.
 

– ‘Yan sanda a Malawi sun ce sun kama akalla mutum 100, bisa zarginsu da hannu wajen far wa wasu da aka yi ikirarin fatalwa.

– A Afghanistan kusan mutane 60 sun halaka a wasu munanan hare haren kunar bakin wake da aka kai a Masallatai guda biyu na mabiya Shi’a a birnin Kabul na kasar.

– Tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya gayyace shi zuwa gasar cin kofin duniya da kasar za ta karbi bakunci a badi.

You may also like