Labarai A Takaice – Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da karfin ofishin sa wajan dakatar da Abdulrashid Maina daga aiki a matsayin sa na shugaban kwamitin kula da Fasho a sakamakon zarginsa da aikata laifi yin sama da fadi kan wasu makudan kudade.

– Gwamnoni 17 daga jihohin kudancin Najeriya ne suka yi taro a karkashin jagorancin gwamnan jihar Lagos, wanda kuma a karshen taron, yace sun amince Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya “madaurinki daya” koda yake akwai bukatar da a sake fasalin kasar.

– Tsohon jagoran sa ido na tarayyar turai a zaben Najeriya na shekarar 2015, Santiago Fisher, ya musanta zargin cewa kungiyar ta fifita takarar Muhammad Buhari bisa sauran ‘yan takarar amma ya yabawa tsohon shugaban kasar Jonathan wanda bai bata lokaci ba ya amince ya sha kaye.

– Umar Abdulmuttalab wani dan Najeriya da ya yi yunkurin tarwatsar da wani jirgin sama dauke da fasinjoji 300 a shekarar 2009 ya shigar da kara kotu kan halin da yake ciki a gidan kaso inda yake daurin rai da rai.

– Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta ziyarci yankin Sahel, ta ce ko shakka babu kasashen duniya za su taimakawa yankin domin kaddamar da rundunar G5-Sahel wadda za ta yaki ayyukan ta’addanci.

– An samu gawar Luka Akechak kwamandan sojojin Sudan ta Kudu da suka yiwa wasu mata na aikin agaji na kasa da kasa fyade a gidan wakafin da yake tsare.

– Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, yace dole ne a yi zaben shugaban kasar da aka shirya yi ranar Alhamis, ko da kuwa akwai ‘dan takarar jam’iyyar adawa Raila Odinga a zaben ko babu.

– Yau ce ranar karrama Majalisar dinkin duniya  wacce aka kafa a shekarar 1945, yanzu tana da wakilai 193 kuma ana gudanar da ayyukanta ne bisa manufofin dake cikin daftarinta.

– Shugabannin cibiyoyin samarda agaji na Majalisar Dinkin Duniya, MDD sun yi wani taro na kwana guda domin neman tallafin Dala Miliyan $434 domin tallafawa mutane Miliyan 1.2 ciki har da ‘yan gudun hijirar Rohingya da masu taimaka musu a kasar Bangladesh.

– Mayakan IS sun kashe fararen hula 116 a garin al-Qaryatayne da ke tsakiyar Syria, lokacin da mayakan ke kokarin tserewa daga farmakin dakarun gwamnati.

– Cristiano Ronaldo ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya na bana da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke bayarwa duk shekara inda dan wasan na Portugal ya sake doke Messi da Neymar.

You may also like